POLITICS:Ganawar Kwankwaso Da Shekaru Ta Tada Hankalin Yan Buhari Da Gandujiyya


A siyasar karnin 2015 zuwa 2019 wannan shine hoton da ya girgiza siyasar Nijeriya da jihar Kano, kuma wannan shine hoton da ake kira kurunƙus karshen zance.

Mai girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ziyarci mai girma Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau a gidan sa dake Asokoro a daren jiya Asabar.

Hakika wannan hoto ya baiwa dukkanin wani mai baki da kunu mamaki, ni kaina da babu kunu a bakina wannan hoto ya bani mamaki sosai, na kuma ji dadinsa kwarai da gaske.
Masu baki da kunu ya kasuwa, yau dai ga Shekarau ga Kwankwaso siyasa ta hadu, maja ta kare, Buhari tattara kayan ka, Ganduje a cigaba da likimo 2019 an fadi zabe da yardar Allah.
#Rariya

Post a Comment

0 Comments