POLITICS: COMRADE MUHAMMAD IBRAHIM IFO YAYI KIRA GA MATASA DA SU ZABI ALI AL'BABA A ZABEN 2019Shugaban yakin zaben HON. ALH ALI ABUBAKAR AL'BABA (G.R.A/KWADO).

COMRADE MUHAMMAD IBRAHIM IFO  yayi kira ga jama'a da matasa baki daya da su goyi bayan HON.ALI ABUBAKAR AL'BABA Dan takarar majilissar jiha mai wakiltar karamar hukumar katsina  a majalissar jiha  a zaben 2019.

COMRADE MUHAMMAD IBRAHIM IFO ya fadi hakan ne a yayin wani taron tattauna da akai da  matasa wanda  da ya guduna  akan yadda za a tafiyar da al'amurran yakin neman zaben  mai zuwa na shekarar dubu da goma shatara wanda ya gudana a ranar asabar ta gabataYa kara da cewa
"Mai girma HON. ALH ALI ABUBAKAR AL'BABA  shine mafi dacewa a jihar mu a halin yanzu kuma ina ganin babu wanda ya fi shi cancanta.


"Na Amince da    Mai girma HON. ALH ALI ABUBAKAR AL'BABA shi kuma na bayyana tun a baya cewa idan har dan  takara muke nema  na gari to ba ko shakkah
Mai girma HON. ALH ALI ABUBAKAR AL'BABA shine yafi caccanta.
"Gashi kuma tun a primary election Allah yayi shine  Dan takarar mu  mafi cancanta wajen jagorancin jihar nan a wannan halin da jihar nan take ciki.COMRADE MUHAMMAD IBRAHIM IFO
ya kara da cewa yana mai kira da kakkausar murya ga mai girma Gwamna RT. HON AMINU BELLO MASARI da kuma shuwaga banni jamiyyar APC  da su kara bada goyon baya ga babban Dan takarar mai wakiltar karamar hukumar katsina a majalissar jiha Mai girma HON. ALH ALI ABUBAKAR AL'BABA duba da cancatarsa da haleyensa masu kyau don cigaban katsina da al'ummar dake  cikin ta baki daya.


Ya kuma ida da cewa yana mai kara rokon matasa da al'umma baki daya da su bada goyon bayan don ga SHUGABA MUHAMMADU BUHARI da kuma RT. HON AMINU BELLO don zarcewarsu a karo na biyu ba don komai ba said don su karasa abin alkhari da cigaba da suka faro. In da akarshe yayi fatan Allah ya tabbatar alkhari.


#NORTHERNFILES TV

Post a Comment

0 Comments