POLITICS:CEWAR HAJIYA FATI RASHIN BADA KAINA A YI AMFANI DA NI YA SA AKA HANA NI TAKARA A PDPRashin Bada Kaina A Yi Amfani Da Ni Ya Sa Aka Hana Ni Takara A PDP, Cewar Hajiya Fati, 'Yar Takarar Majalisar Jihar Gombe Ta Kudu'Yar takarar majalisar jihar Gombe ta Kudu a karkashin jam'iyyar PDP, Hajiya Fati Gombe ta danganta rashin tantance ta a matsayin 'yar takara da rashin bada kanta a yi amfani da ita da wasu gurbatattun jagororin jam'iyyar suka bukaci hakan.


Matashiyar 'yar takarar, wadda kuma mawakiya ce, ta bayyana cewa duk wasu sharruda da dan takara yake cikawa ita ma ta cika su, amma ta yi mamakin yadda masu kwamitin masu tantance 'yan takarar suka ji amincewa da ita ba tare da wasu kwararab hujjoji ba.


"Ba zan yi mamaki ba don an ki tsayar da ni takara, saboda akwai daya daga cikin membobin da suke tantance 'yan takara da ya nemi na zo na same shi a otal ko kuma na ba shi cin hancin dubu dari kafin a tantance ni".


"Ina da shaiduna domin a lokacin da ya nemi na zo na same shi otal din na yi rekodin maganar da muka yi, wanda nan gaba zan bayyana duniya tare da fadin sunansa".


Hajiya Fati wadda ta kashe makuden kudade daga aljihun ta domin yakin neman zabe, sakamakon kin tsayar da ita takarar, dubban mata da matasa dake yankin sun yi barazanar kin fitowa su yi zabe saboda kin tsayar da ita takara da PDP ba ta yi ba.

Hazikar mawakiyar, wadda take da gidauniyar tallafawa mata, inda take kai ziyara gidajen marayu, asibitoci da tallafawa marasa karfi, ta kuma ja hankalin Gwamna Dankwambo na jihar Gombe da uwar jam'iyyar PDP ta kasa da su yi gyara a cikin jam'iyyar kasancewar akwai gurbatattu a cikinta.
Manazarta na ganin cewa rashin baiwa Hajiya Fati kujerar takarar babbar asara ce gare ta sakamakon makuden kudaden da ta cire a aljihunta wajen yin hidindimun takara.

  HOTUNA

KADAN DAGA CIKIN IRIN AYYUKAN DA MATSHIYAR YAR TAKARAR TA GUDANARPost a Comment

0 Comments