CELEBRITIES : TURKASHI !!! Mansurah Isah Ta Tona Asirin Mata Ƴan Fim

 
TURƘASHI Mansurah Isah Ta Tona Asirin Mata Ƴan Fim


...wata ma kowa yasan Ƴar Maɗigo ce, inji Mansurah


Bayan ɓullar wasu hotunan Rahama Sadau wadda suka jawo cece-kuce a kafafen sadarwa, da yawa daga cikin mata ƴan fim sun fito suna caccakar Rahama Sadau ɗin, inda ta kai wasunsu har da yin kuka.


Sai dai Mansurah Isah tace duk kukan munafurci suke yi, inda tayi musu tonon silili a shafinta na Instagram, ta bayyano wasu daga cikin irin laifukan da suke aikatawa, kamar yadda zaku gani.


Mansurah Isah tace:-


"Wallahi da banso nayi magana ba, amma kunsa saida nayi magana, wannan shirmen ya isa haka. Naga wata ma da ta fito daga Police Station kwanannan tana wa'azi, mtsww".


"Wata da ta wallafa nonuwanta tana rawa a status itama wai tana wa'azi, wata ma da kowa yasan Karya ce (Ƴar Maɗigo) itama tana wa'azi. Kun gani ko dukkan ninmu masu zunubi ne, sannan munfi tsoron mutane akan tsoron Allah a zuciyar mu, amma zamu fito kafafen sadarwa mu nuna mu na Annabi ne".


"Kowacce in za tayi magana sai ta saka Hijabi, wa ku ka yaudara? Kuje ku duba shafukansu ba saka Hijabi suke ba. Allah na kallon kowa, ku cigaba Allah na kallon mu dukkan mu, shin duniya ce zatai muku hisabi?"


"Dukkan ku kun samu wata dama ce ta fito da abinda yake cikin zuciyarku. A gurin Allah ne kaɗai zan nemi yafiya, kuma shi kaɗai zan yiwa kuka a ɓoye ko a fili a lokacin da nasan na aikata laifi kuma nasan cewa banyi daidai ba".


"Wannan ya isheni ishara, ALLAH YA NA SON mai neman gafararsa koda sau nawa zai aikata laifi kuma ya nemi tuba".


"Ku saka wannan a kanku ku daina damun mu da wani shirmen bidiyon ku na banza". Inji Mansurah Isah

Post a Comment

0 Comments